Dalilin da ya sa ake neman wannan matashi
Akwai wata rigimar da al'ummar garin Barama su ke yi da Shugaban karamar hukumar Gwandu Local Govt, Alh Shehu Bagudu Dalijan,
Wanda da Shugaban karamar hukumar Ya fara Tauyewa Mutanen garin Barama wadanda lokacin Damina Anyi Iska Kwaninka Rufi na al'ummar garin suka kware, Anyi Anbaliyar Ruwa Tsakiyar Garin Barama da gidajen Su Duk Sun cika Da Ruwa, Anyi Kusan Kwana Arba,in Ruwa Ba su Janye A Tsakiyar Garin Barama ba, Gidaje Su ka Rurushe shi kansa matashin da ake kokarin kamawa yanzu akwai Ciki Da Falo Ko Shigarsu Bai Ba Amma ruwan sun roshe su.
Dakunan da suka rushe sunfi dari a lokacin. Har yanzu wasu basu samu Damar gyarawa ba saboda rashin abin gyara, Wanda shi Shugaban bai je ko jaje ya yi wa al'ummar garin ba kuma bai aika ba a yi masu ba.
Mai girma Gwamna ya turawa Gwandu local Govt tallafi akan a rabawa wa Wadanda Iftila,in da na lisafa Ya shafa amma abin mamaki ko Magajin Barama Bai san anyi ba. ma'ana dai babu mutun ko Daya daga cikin Barama da ya samu Wannan Tallafin, wannan matashin na sane amma ban fadawa duniya ba,
Haka zalika mai Mai Girma Gwamnan jahar Kebbi ya bayar da kwangilar hanyar da ta tashi daga Gwandu Tabi Ta Barama ta wuce Argungu. Al'ummar garin garin Barama Ba su masan da an yi awon hanyar ta bi ta garinsu ba. Sai dai suka tashi da safe suka ga awo Ya biyo Ta garin Barama amma sai wani Kauye da ke kusa da garin da ya ke su ke da manyan 'yan Siyasar da aka sani, suka turo yaran su cikin dare suka ciccire Itacen awon hanyar suka mayarda Su Can kauyensu.
Daga nan rigima ta Tashi, al'ummar garin Barama ba mu dauki matakin daukar doka a hannu ba, su kaje gun Chairman su ka sanar da shi halin da ake ciki ya zo dakansa ya ga yadda Abin yake ya ce Wadancan 'yan kauyen ba su da gaskiya dan haka aiki nan Barama za a yi shi saboda nan awo yabi. Har Rantsuwa Takai uku ya yi Muna Akan Ba za a dauke aikin nan daga Barama ba.
Amma sai dai kash! Bayan sati biyu zuwa 3 sai ya dawo tare da Wadancen 'yan Siyasar Kauyen da aka sani.
Za su dauki motocin aikin hanyar su mayar da su Wancan kauyen ba tare da Wani kwakkaran bayani ba. Dan haka al'ummar garin Barama su kace Ba su Yarda ba abin ya zan Rigima. Har shi Shugaban ya yi ikkirarin sai dai duk wanda a cikin Barama ya kare amma ba makawa sai ya dauki motocin ya mayar da su wajen masu galihu. sut kuma suka ce sai dai ya kashe su din kamar yadda ya yi ikirarin yi, amma ba za su yarda a dauki motoci ba, daga Inda Gwamnati ta aje su a mayarda su inda batasan da can ba.
Daga karshe dai ya koma ya zo da Motacin 'yan sanda sun kai 16 Su kayi Ta Halbe-Halbe cikin garin Barama. Sai dai babu wanda ya kula su. Sai dai matashin da ake kokarin kamawa yanzu haka kafin jami'an su zo. An tabbatar masa da cewa ba Wanda ya isa canza alkiblar da aka bayar da kwangilar kan Hanyar. Dan haka jami'an tsaron su ka gama harbe harbensu su ka yi gaba domin matashin ya Sanar da al'ummar garin ko da Shugaban ya dawo daukar Motar Su kyaleshi kawai Saboda ba shi ne dankwangilar hanyar ba, kuma ba Dan kwangilar ya turo shi ba wannan dalilin ne ya hana a kashe mutanen garin Barama, duk da haka matashin bai shedawa Duniya ba.
Yanzu kuma ya dawo maganar dajin Da ya tabbatar da da shi mutanen Barama suka Dogara, Saboda Ya Kuntata wa al'ummar garin Barama, ya baiwa fullanin da ba sufi su 20 ba Dajin.
Bayan kuma duk inda ya kamata su tafi saboda ayi masu sulhu tsakanin su da fullanin nan sunje Amyma anki azo a sulhunta su, su zauna Lafiya ko dan zaben da ke tafe.
Dan haka mutanen kauyukkan da suka shafi karamar hukumar Argungu da Gwandu sunka yi zama akan Cewa a raba hulda da fullanin. Kar a saya gare su kar a sayar masu, kar a shiga Mota daya Dya su idan kuma sun mutu kar a tafi Janaiza Bale Gaisuwa.
Ganin wannan hukunci ya sa matashin ya yi Video tare da Hotuna ya yadawa duniya Domin mahukunta su shigo cikin lamarin su sulhunta su a zauna Lafiya. Domin wannan mataki da al'ummar wannan yanki suka dauka zai iya yin Jagoranci zuwa ga Haihuwar wata Mummunar gaba da Allah dai ya San Inda za ta tsaya. Kuma al'ummar yankin ba za su iya KASHE TA ba. Domin Hakan dai zai sa wadanda abun ya shafa sugani su sa aje a yi masu bincike.
Lokacin da bidiyon ya yadu a duniya labari ya riski Chairman ya nuna baisan wainar da ake toyawa ba. Dan haka ya ce sai Ya bincika. Bayan ya Bincika ya ga Labarin da Videon sai yasa a kira daya daga cikin mutanen Barama a yi Sulhu. Bayan ya je sai ya sa Dpo na Yan sanda (police) Ya kulle shi. Yau kwana 3 kenan anyi ta zuwa Dpon yaki bayarda shi. Ya ce Chairman ya ce a rike mai shi, sai ya neme shi. Yanzu kuma ya baiwa Dpon umarnin ya kamo matashin duk inda yake Tunda shi ya watsa labarin. Sannan azo ayi sulhun rigimar da zata Iya kawo fadan kabilanci,
Wannan shi ne laifin wannan matashi. Yanzu Haka dai bayan wanda suka tsare Tun shekaranjiya, yau ma Dpo ya kira matashin Inda ya sheda masa za su rike Magyajin Barama har sai matashin ya mika kasa.
Wanda Hakan ya sa wannan matashi Mai suna Aliyu Usman Barama Ya ke Sanar da Duniya da yan uwa 'yan Social Media da manyan yan siyasarsu Idan suka daina ganin postings dinsa to Sun kamanm shi.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
20-1-2019


