Masu ZANGA-ZANGAR dai sun fito ne domin nuna rashin amincewarsu ga matakin Gwamnan #Kano Abdullahi Ganduje na rattaba hannu a kan sabuwar dokar kafa sababbin masarautu guda hudu da suka hada da Rano da Karaye da Gaya da kuma Bichi.
Jahar Kano dai ita ce jaha mafi yawan jama'a a arewacin najeriya tare kananan hukumomi 44. Jahar tana da sarki Mai daraja ta daya Guda daya tilo. Wanda shi ke Jagorantar sauran hakimmai na dukkanin jahar. Sai dai kwatsam yanzu an wayi gari da ganin 'yan Majalisar jahar sun fito da kudurin kirkiro Masarautu hudu. Wanda yau Gwamna Ganduje ya Sanyawa dokar hannu.
ZANGA-ZANGAR da ta kun matasa maza da mata, sun nemi Gwamnatin jahar ta maida hankali wajen samawa matasa ayukkan yi da kirkiro shiraruwa da za su bunkasa jahar. Ba wai kirkiro Masarautu ba. Da za su kassara jahar da kuma daidaita ta.




