MAKOMAR JAHAR ZAMFARA GOBE A KOTUN ALLAH YA ISA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 15 May 2019

MAKOMAR JAHAR ZAMFARA GOBE A KOTUN ALLAH YA ISA!


Gobe ne in Allah ya Kai mu, kotun kolin Najeriya, kotun da in ta yi maka ko ba daidai ba, sai dai Allah ya isar maka da isarsa! Ta cigaba da sauraren kararar da bangaren Gwamnatin jahar Zamfara, su ka shigar akan cewa tabbas hukucin da wata babbar kotun Shari'a ta jahar Zamfara cewa jam'iyar APC ta yi zaben fitar da gwani Wanda ya cilastawa hukumar zabe karbar yan takararsu gaskiya ne. Hukucin da kotun daukaka Kara da ke zamanta a Sokoto ta jingine. Hukucin dai shi ne ya hana baiwa 'yan takarar APC da na 'yan Majalisar jaha da Gwamna da mataimakin da su ka lashe zabe, shedar lashe zaben.

Wannan shi ne zama na biyu Wanda za a yi gobe alhamis 16-5-2019. Duk da ba a tsammanin yanke hukuncin a ranar kuma a gun. Sai dai zaman zai zama kusan shi ne kashin Bayan Shari'ar domin zama na uku ana tunanen shi ne na yanke hukunci!

Hakaki wannan shari'a Tana da tasiri ga dukkanin al'ummar jahar Zamfara. Da dama na son a soke damar da aka baiwa 'yan takarar APC. Wasu kuma na son a tabbatar da halaccin zaben Wanda zai baiwa dan takarar da ya lashe zaben Mukthar Shehu Idris. Zama Gwamnan jahar Zamfara. Ya Dora daga Inda mai gidansa Gwamna Abdul'azizu Abubakar Yari, ya sanya aya.

Allah ka ka halacci adalci ka umurci bayinka su yi wa junansu, Allah Kai ka halacci zaluci baka yi kuma ba ka son a yi, Allah Kai ka halacci Gaskiya ka ke yiwa bayinka umurni da su RIKE ta.

ya Allah Shari'ar gobe, ka Dora masu gaskiya akan gaskiya. Allah ka dorawa Zamfarawa shuwagabannin kirki, da za su tsamo su daga cikin halin ni-'ya-sun da su ke ciki.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
15-5-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here