MATAIMAKIN GWAMNAN ZAMFARA, YA BAYAR DA TALLAFI NA BAN MAMAKI, GA MABUKATA - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 18 May 2019

MATAIMAKIN GWAMNAN ZAMFARA, YA BAYAR DA TALLAFI NA BAN MAMAKI, GA MABUKATA














Ganin yadda lokacin siyasa ya wuce har wasu 'yan siyasa su ka yi Hijira. Tare da tushe duk hanyoyin da za a iya ganinsu balantana rabarsu. Wanda Hakan ya taimaka gwarai wajen jefa Al'umma a cikin wani Hali, musamman a cikin wannan watan na Ramadan da 'yan siyasa kan baje kolin manufofinsu ta hanya raba kayan masarufi ga mabukata.



Kamar kullum a wannan shekarar da kakar Zabe ta gwanta dama. 'yan siyasar jahar Zamfara su ka kasa gane Gabas Hakan ya sa mafi yawansu sun matse bakin aljihunsu. Sai dai abun mamaki kwatsam sai aka ga mataimakin Gwamnan jahar Zamfara, Wanda tuni wasu suka Anya da cewa karshen siyasarsa ya zo. Ganin yadda ana yi ta Kai ruwa Rana tsakanin Gwamna Mai ci-a-yanzu da shi, Wanda Hakan ya haifar da tsamin dangantaka da ta kai ga Dena ganin mataimakin Gwamnan wajen kowane Aiki da ya shafi Jagoranci ko wakilcin gwamnati. Amma yau ya fito da atamfofin da ko shi bai San iyakarsu ba. Ya baiwa mabukata. Sai dai ni da ke wurin na Shedi an kwashe sama da awanni uku ana rabawa mata atamfofi. Kuma wannan ita ce kyauta mafi yawa da na taba ganin ya bayar a lokaci daya tun hawansa kan karagar mulki. Duk da duk Shekara yana bayarwa  kwarai da ga mabukatan a wannan sai dai na wannan lokacin yawansu ya yi yawa.

Kuma kamar yadda ya fada wannan na mata ne kurrum akwai na yara kanana da kuma maza.

Muna fatan Allah ya Saka masa da alheri ya baiwa 'yan siyasa da masu hannu da Shuninmu ikon koyi da shi wajen taimakon Al'umma.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here